3 Afirilu 2026 - 21:59
Source: ABNA24
Iran Ta Sake Kakkabo Jiragen Yakin Amurka Ciki Har Da Nau’in F35 A Karo Na Biyu

Mai magana da yawun babban hedkwatar Hazrat Khatamul-Anbiya (SAW) ya sanar da kakkabo jirgin yaki na F35 a karo na biyu wanda shine mafi ci gaban jirgi a Amurka bisa anfani da nau’rorin tsaron saman dakarun IRGC.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Jirgin saman yakin Amurka nau’in F35 na zamani na biyu na zamani na tsatso na biyar an lalata shi a tsakiyar sararin samaniyar Iran ta re tabbatar da fadowarsa sa. Sakamakon mummunar fashewar jirgin a lokacin fadowar shi akwai yiwuwar matukin jirgin ya bace.

Bayana hakan an ga jiragen Amurka na yawo domin neman matukin jirgin da ya fado. A cewar bincike, Amurkawa na neman matukin jirgin yaki da sojojin Iran suka ka kakkabo a safiyar yau ta cikin wasu jirage masu saukar ungulu na Blackhawk, wani jirgin sama na Hercules 130, da kuma jiragen leken asiri. Matukin jirgi na yaƙi yawanci ana haɗa su da GPS waɗanda za a iya gano su yayin da suka fado. Sai dai yankin da Amurkawan suka yi nazari a kai ya nuna cewa ba su san ainihin wurin da matukin nasu yake ba kuma suna nemansa ta wasu hanyoyi.

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha